DIGITAL SKILLS 10 WADANDA YA KAMATA MATASAN AREWA SU KOYA A SHEKARAR 2024

Ko kun san akwai yiwuwar manyan kamfanonin America su fara kawo reshensu nan Arewa kamar su Amazon?

Hakan yana nuna lallai matasan Arewa za su samu damammaki amma ga wadanda suke da kwarewa a digital skills.

Duba wasu digital skills guda 10 wadanda ya kamata matasan Arewa su mayar da hankali a kai a wannan sabuwar shekarar.

DIGITAL SKILLS WADANDA AKE BUKATA

🔷Web Development
Wannan skill din yana koyar da yadda ake coding don gina shafin yanar gizo ta hanyar amfani da programming languages irin su HTML, CSS da JavaScript, PHP da SQL. Idan ka iya wannan skill din za ka zama Web Developer. Wannan skill din zai fi kyau ga wadanda suke da computer.

🔷Digital Marketing
Ilimin sanin hanyoyin da ake amfani da su don tallata kasuwanci ko hajoji da zamanantar da shi a yanar gizo. Ana bukatar Digital Marketer ya iya Social Media Marketing; dabarun tallata hajoji a dandanlin sada zumunta irin su Facebook ko Instagram, Content Marketing; dabarun tallata hajoji ta hanyar sharing digital content irin su hotuna ko bidiyoyi, da sauransu. A yanzu haka kamfanonin Kudancin Nigeria har da Arewa suna bukatar wadanda suka iya wannan skill din don yi musu aiki. Za ka iya koyensu duka da wayarka ta hannu.

🔷Social Media Management
Wannan skill din kuma shi ne yadda ake managing social media accounts (Facebook, Twitter, Telegram, WhatsApp, TikTok, Instagram etc.) na kamfanoni, ‘yan siyasa, ko celebrities don yi musu aiki su rinka biyanka. Wayarka ta hannu ta ishe ka aiki.

🔷Affiliate Marketing
Ilimin sanin dabarun fara kasuwancin kamasho wato affiliate marketing da yadda za ka zama affiliate marketer. Affiliate Marketing shi ne yadda za ka gayyato mutane su sayi kaya a wani kamfani, shi kuma kamfanin ya biya ka kamasho, misali 10% a duk mutum daya wanda ya musu ciniki ta hanyarka.

🔷Amazon KDP
Wannan skill ne wanda yake koyar da yadda ake bude Amazon Kindle Direct Publishing da yadda ake samun kudi da shi. Zai fi dacewa ga wadanda suke sha’awar rubutu don sarrafa basirarsu don samun kudi a yanar gizo.

🔷Dropshipping and Online Arbitrage
Dropshipping shi ne yadda ake sayo kaya daga kasashen waje sannan a sayar da su a nan wurarenmu. Online Arbitrage kuma shi ne sayo kaya daga wata kasuwa sannan ka sayar a wata kasuwa saboda bambancin farashi. Misali, ka sayi kaya a Jumia sai ka kai Amazon ka sayar. Ko kuma ka sayo kaya daga AliExpress sai ka kawo Jumia ko Jiji ka sayar.

🔷UI/UX Design
Yadda za ka koyi creative designs masu kayatarwa kamar su hotuna da kuma tsara front-end design na shafuka da kayata tsarin wasu digital products ta hanyar amfani da computer. Wannan wani skill ne wanda manyan kamfanoni suke bukatar kwararrunsa, saboda zai taimaka musu wajen kirkirar creative designs na shafukansu, sannan bugu da kari graphic designs na tallace-tallacensu.

🔷Cyber Security
Koyon tsaron na’ura da yanar gizo, inda za ka koyi tsaron na’ura, asusau, manhajoji, ko shafukan yanar gizo. Shi wannan skill din, in ji wani masani, ya zama wajibi ga duk wanda yake ta’anmuli da wayar hannu ko na’ura, saboda zai taimaka maka wajen sanin yadda za ka tsare asusanka daga kutse, kasancewar ya zama ruwan dare a yanzu.

🔷Copywriting
Yadda ake tsara rubutun tallace-tallace irin su sales letter, email campaigns, da ingantattun dabaraun da ya kamata marketer ya sani. Duk abun da kamfanoni suke rubutawa na tallace-tallace, to hakika Copywriter ne yake tsarawa. Shi ne wanda yake da kwarewa wajen tsara rubutun talla. Da wayarka ta hannu za ka iya koya a Flowdiary. Sunan course din Copywriting 101: An Ultimate Writing Technique.

🔷Content Creation
Koyi yadda za ka yi creating digital content irin su video, audio, article don zama content creator da wayar hannu. A nan, kana bukatar sanin Graphic Design da Video Editing. Cikin sauki duk akwai su a Flowdiary. Za ka iya shiga courses guda biyu kacal sun ishe ka kwarewa a wannan skill din, ga su kamar haka: Content Creation 101 da kuma Smartphone Graphic Design.

Abun farin cikin shi ne, Flowdiary za ta koya maka duk wadannan tarin skills din a harshen Hausa cikin sauki.

KANA SON FARAWA?

Shiga Play Store ka sauke app dinmu mai suna Flowdiary sannan ka yi register 👇

Invitation code: 7738383

Sai ka shiga ka zabi course din da kake so ka fara nan take.

KANA BUKATAR KARIN HASKE, RECOMMENDATION, KO TATTAUNAWA DA MU?

Tuntube mu ta WhatsApp

Za mu taimaka maka wajen zabar course din da zai dace da kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *