A takaice, idan kana son shiga harkar fasaha don a dama da kai, ka bi wadannan matakan 👇

✔ Ka sa a ranka za ka iya

✔ Ka zabi bangare domin akwai bangarori kala-kala a fannin fasaha, misali: web development, app development, graphic design, digital marketing, data analysis, AI, da sauransu. Mentor zai taimaka maka wajen zabar abun da zai fi dacewa da kai

✔ Ka nemi mentor wanda zai kama hannunka ya nuna maka abun da ya dace, ya rinka ba ka shawarwari da kuma guiding dinka, saboda shi ne wanda ya je matakin da kake son zuwa ko kuma ya kama hanya, ka ga dole ka bi shi don shi ya san hanyar

✔ Ka koyi skills kala-kala har ka gano inda ka fi so

✔ Kar ka yi gaggawa, ka bi komai a sannu tare da jajircewa da kuma hakuri, sannan kada ka zama dan sha-yanzu-magani-yanzu

✔ Ka “auri bincike”, ya zama cewa ba ka da wani babban aboki face bincike. Ka tambayi Google, ChatGPT, masana, mentors, da sauran abokan gwagwarmaya

✔ Ka fara aiwatar da abubuwan da kake koya

Flowdiary ta kawo muku saukin duk wadannan matakan cikin harshenku na Hausa. Za mu koya maka skills, sannan mu ba ka sannan mentorship kyauta.

Abun da muke bukata a wajen shi ne la fada mana me kake so? Mu kuma za mu taimaka maka don shiga harkar fasaha’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *