Cyber Security ilimi ne na zamani da ke koyar da yadda ake bayar da tsaro ga na’urori, shafukan yanar-gizo, da kuma manhajojin yanar-gizo.

Mutane a wannan zamani suna karantar cyber security don samun kwarewa a fannin ilimin tsaron na’ura da yanar-gizo. Kamar sanin cikin da wajen na’ura da sanin sirrikan ba ta tsaro da kariya daga masu kutse ko cututtukan da ke iya hargitsa ta.

Akwai manya-manyan cyber security analysts, wato kwararru a fannin tsaron bayanai da na’ura da suke taimaka wa ma’aikatu da gwamnatoci wajen tsare bayanansu da kadarorinsu na yanar-gizo, da kuma samar da tsaro ga tattalin arzikin cikin kasa da ake samu ta hanyoyin sadarwa na yanar-gizo.

Musamman a wannan lokaci na digital da ilimin na’ura ya mamaye duniya da harkokin kasuwanci, wannan ya sa muke amfani da computer da kuma yanar-gizo wajen ci gaba da tafiyar da ayyukanmu, kuma muke amfani da su wajen adana dukiyoyinmu da sirrikanmu.

Wannan dalili na samuwar fasahohin na’ura da yanar-gizo ya sa ma’aikatu da hukumomi suke bukatar wandanda suke da kwarewa a fannin ilimin cyber security domin su taimaka masu wajen bayar da tsaro ga na’urorinsu da bayanansu da ke ajiye a yanar-gizo.

Idan kana son zama masani a bangaren cyber security da kwarewa a fannin, to a manhajar Flowdiary an ajiye wannan course na cyber security bisa tsari mai kyau da yarenka na Hausa ta yadda za ka ji dadin koyo da fahimta yadda ya kamata.

2 thoughts on “Me Kake Son Sani Game da Karatun “Cyber Security” da Kuma Fa’idarsa a Yau?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *