Flowdiary Jobs

Don karfafa wa ‘yan’uwanmu matasa gwiwa, ba mu tsaya a iya koyar da digital skills a makarantarmu ta yanar gizo Flowdiary ba, mun kawo tsarin Flowdiary Jobs.

Wannan sabon tsarin zai ba wa daliban Flowdiary damar cike guraben ayyuka daban-daban sannan mu kuma mu hada su da kamfanonin da suke neman ma’aikata don su yi musu aiki a biya su.

A koya maka skills sannan a ba ka damar nuna wa duniya skills dinka don a dauke ka ka yi aiki a biya ka, wannan goma-ta-arzikin duk Flowdiary ce ta tanadar.

Da farko ya kamata mu san sharuddan da ake bi kafin cikewa, su ne kamar haka:

  1. Dole sai ka kasance dalibin Flowdiary wanda ya karanci course (amma ban da GEN-101)
  2. Dole sai Points dinka ya haura 100, ta hakan ne za a gane ka bibiyi darussa kuma ka iya wannan abun

YADDA ZA KA CIKE

  1. Ka shiga account dinka ta web version, wato ta website dashboard dinmu yanzu ta nan
  2. Ka danna navigation button kamar yadda yake a sama, sannan ka shiga Menu sai kuma ka danna Apply for Job sannan ka cike bayananka kamar su:

i. Job Title: wato matsayin aikin da kake son cikewa

i. How do you work: yadda kake aiki (online ne ko offline ko duka) saboda idan za a dauke ka aiki a san tsarinka

iii. Skills: za ka zabi skills din da ka fi iyawa akalla guda biyar

iv. How much do you charge: nawa za a biya ka a wannan aiki

v. About me: bayani game da kainka, a nan ana so ka rubuta ayyukan da ka yi a baya (idan akwai), da kuma yarukan da kake ji misali Hausa, English, Arabic, dss

vi. Email Address: za a iya tuntubarka ta email address

vii. WhatsApp Number: haka nan za a iya tuntubarka ta WhatsApp

viii. Social Media Links: sai na karshe shi ne social media profile links dinka irin su Facebook, Linkedin, da Twitter. Misalin link din da ake bukata shi ne kamar haka: https://facebook.com/mohiddeenahmadd

Sannan sai na karshe kuma za ka yi accepting na terms and conditions din Flowdiary game da tsarin freelancing. Yana da kyau ka shiga ka karanta wadannan tsarukan don za su taimaka.

Mu kuma daga nan za mu gayyato kamfanoni, kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), ko sauran mutane don su duba wadanda suke so su musu aiki sai su tuntube su.

Za ku yi musu aiki ne a matsayin freelancers, amma idan suka ga ayyukanku sun yi kyau to za mu daukarku aiki na dindindin a wurarensu. Don haka sai a tsaya a yi abun da ya dace.

Ka yi sani cewa sabanin sauran shafukan baje kolin ayyuka, ko sisi Flowdiary ba zai karba a hannunka ko hannun wadanda za ka yi wa aiki ba.

Abu na biyu shi ne mu lura da kyau wajen cikewa kada mu yi gaggawar sanya wasu abubuwa a inda ba su dace ba ko kuma wuce wasu wurare.

Za ku iya shiga nan don ganin duk ayyukan da ku ka cike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *