Flowdiary content marketingFlowdiary content marketing

Content Marketing wani ilimi ne da ake amfani da shi a lokacin da ake tafiyar da kasuwa ko sana’a a kan tsarin digital marketing, ta hanyar da hakan ke taimakawa wajen amfani da duk wani nau’i na content kamar hotuna, bidiyoyi, sautuna, rubuce-rubuce da sauransu don tallata wadannan kayayyakin ko wannan sana’ar.

Duka wadannan abubuwa da na lissafa za ka iya zama kwararre dan kasuwa a kansu ta hanyar sanin ilimin content marketing.
A takaice dai content marketing shi ne dabaru da hikimomin kasuwa wajen iya sarrafa harshe ko rubutun da ke janyo ra’ayin mutane zuwa a kan wata kasuwanci da take zahiri ko kuma a yanar-gizo.
Akwai manyan-manyan kwararru a bangaren content marketing da suke taimakawa musamman ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa, su na yi masu aikin da za su samu cigaba a harkokin kasuwancinsu ko na siyasa.


Daga karshe kai ma za ka iya zama kwararre a fannin content marketing ta hanyar shiga makarantar yanar-gizo ta Flowdiary. Domin muna koyar da wannan kwas na content marketing a kan farashi mai sauki. A inda za a koyar da kai yadda ake kirkirar rubuce-rubuce na kasuwanci, da hanyoyin da za ka yi amfani da su wajen tallata kasuwarka.

One thought on “Yadda Za Ka Yi Amfani da Digital Contents Don Bunkasa Kasuwancinka a Yanar Gizo”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *