Flowdiary MentorshipFlowdiary Mentorship

Babban albishir din da muke yi muku a wannan watan shi ne gabatar muku da “Flowdiary Mentorship”, tsarin bayar da horon mentorship ga daliban Flowdiary kyauta.

Ba koyar da karatu kadai muke yi a Flowdiary ba, za mu yi mentoring dinka don tabbatar ka koyi abun da kake karanta tun daga matakin ‘yan koyo (beginners), zuwa matakin matsakaita (intermediates), har zuwa matakin kwararru (advanced).

Mun kawo wannan tsarin mai suna FLOWDIARY MENTORSHIP a matsayin saukakkar hanyar mu’amala tsakanin dalibai da malamai don fahimtar juna, bayar da horon mentorship kyauta, da yin cudanyar karatu da taimakon juna a tsakanin dalibai.

ABUBUWAN DA MENTORSHIP YA KUNSA

  1. Malaminka zai zama maigidanka (mentor), zai daura ka a hanyar abun da yake ganin ya dace
  2. Malami zai ba ka shawarwari masu kyau
  3. Malami zai ba ka recommendations na wasu littatafai, rubuce-rubuce, courses, ko wasu bidiyoyi
  4. Malami zai nutsar da kai a kan daidai da akasinsa
  5. Malami zai amsa maka tambayoyinka
  6. ‘Yan’uwanka dalibai za su ba ka shawarwari, ko recommendations, ko ba ka tutorials

KA’IDOJIN MENTORSHIP

  1. Akwai timetable na Mentorship Session a wannan tsarin. Kowanne Mentor/Malami akwai lokacin da zai gabatar da mentorship
  2. Kada ka kira malami ta waya saboda yawan schedules, ka jira lokacin mentorship idan ya yi sai ka tura sakonka
  3. Idan malami bai amsa maka da wuri ba kada ka yi fushi, ka yi sani cewa shi ma yana da uzuri kala-kala kuma yana fama da sauran dalibai
  4. Dole ka karance kana karantar course din malamin kafin ya ba ka mentorship
  5. A ka’ida, a tsarinmu ba a yin gaggawa. Ka kwantar da hankalinka a matsayinka na mai koyo, ka bi darussa a hankali ka koya idan ba ka gane ba sai ka yi tambaya
  6. Akwai dalibai da dama wadanda kuke karantar course iri daya, ku yi taimakekeniya a tsakaninku
  7. Kada ka turo link ko wani abun da bai shafi Flowdiary ba
  8. Idan kana da wani project wanda kake so mentor dinka ya yi guiding dinka a kai, za ka iya tuntubarsa ka tura masa privately ba sai a mentorship forum ba

Mentorship Timetable

YAYA AKE SHIGA?

Ka shiga Flowdiary Dashboard dinka ka duba navigation button, za ka ga Mentorship ka danna, nan take zai kai ka mentorship forum din

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *