FlowdiaryFlowdiary

Watakila ka dauki shekaru kana fama da wani abu amma ba ka sani ba ya dace da kai ko akasin haka.

Idan haka ne, jarraba wadannan hanyoyin ka gani 👇

1 — DISCOVER YOUR TALENT

Ka gano baiwarka, domin kowa yana da baiwa ta musamman. Sanin baiwarka shi zai taimaka maka wajen yin abun da ya dace da kai.

2 — KNOW YOUR LEVEL

Ka san matakin da kake da kuma matakin iliminka. Shin me za ka iya yi?

3 — TRY DIFFERENT THINGS

Ka jarraba abubuwa kala-kala, kada ka tsaya a guda daya. Wannan ne zai sa ka gano abubuwan da watakila za su kwanta maka a rai.

4 – DISCOVER WHAT YOU LIKE MOST

A cikin abubuwan da kake jarrabawa, ka fahimci wanne ne ya fi kwanta maka a rai kuma mene ne dalili

5 — CHANGE PLANS

Ka rinka canja tsaruka don cimma nasara a abubuwan da ka sa a gaba. Ka jarraba Plan A, idan ya ki ka koka Plan B, idan ya ki ka koma Plan C, idan ya ki ya jarraba Plan D, daga nan ka zarce Plan E, idan ba ka dace ba ka dawo baya.

6 — IMPLEMENT MOST

Ka rinka aiwatar da abubuwan. Kada ka bar su kawai a matsayin ideas, saboda idea ba ta aiki ba tare da an aiwatar da ita ba.

Ku yi sharing wasu ma su amfana.

#FlowdiaryApp #LearnOnFlowdiary

One thought on “TA YAYA ZA KA SAN ABUN DA YA DACE DA KAI?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *