Jack Ma ya ce a lokacin da kake shekarun 20s ka yi kokari ka samu wani kwararren maigida ka koya daga gare shi, kar ka damu da kudin da za ka samu, kai dai kawai ka koyi abun.

Ka kwatanta kanka a matsayin wanda ya je koyon gyaran mota a gareji, ka ga abun da yake gabanka kawai shi ne yadda za ka koyi aikin, ba wai kudin da za a rinka ba ka a matsayin sallama ba.

CEO ya ce, shi ya sa duk lokacin da na tuno da wannan darasin babu wanda yake fado min a rai sai wani yayanmu mai suna Mohammed Yahaya Mohammed, wanda tsarinsa yake matukar burge ni.

Ya yi aiki na tsawon shekaru a wani kamfanin kasar waje wanda yake da branch a Nigeria, ya samu experience kwarai da gaske, daga nan shi ma ya dawo gida ya bude nashi kamfanin.

Kamfaninsa mai suna Fast Star Express Logistics Ltd., kamfanin delivery ne da ke cikin garin Kano wanda yake isar da sakonnin al’umma a lungu da sako har zuwa wasu jihohin.

Na tabbatar experience din da ya samu a wancan wajen da ya yi aiki ne yake taimaka masa, saboda ya san business din sosai. A lokacin da yake aiki da su ya nutsu kwarai ya koyi abun da ya dace, yanzu ga shi yana cin gashin kansa tare da mutanen da ke karkashinsa.

Don haka kai ma ka dage Malam, ka je ka koya a wajen kwararru kada ka ce kudi kake nema lokaci daya, tabbas hakan babban kuskure ne. Duk girman kamfani ko bukatarsa gare ka ba zai yarda da kai ba matukar ka nuna kudi kake so ka samu kawai.

Kuma duk wanda ka gani a babban matsayi tabbas wahalhalun da ya sha a baya ne suke paying yanzu, kada ka yi tunanin zuwa babban mataki lokaci daya.

Allah Ya taimake mu, amin.

One thought on “SHAWARAR JACK MA GA MATASA: ABUN DA YA KAMATA MU DUBA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *