Tabbas akwai tarin abubuwa wadanda ba a yi idan aka je interview ta neman aiki, ga wasu daga ciki na tsakuro mana don mu kula da su:
- Da zaran ka shiga wajen kada ka nuna halin manyanta ko ‘karanta, kada ka nuna kamar kana neman a taimake ka a dauke ka aikin nan; haka nan kada ka nuna ka fi karfin wurin
- Idan ka shiga wajen da ake zama don jira, kada ka saka wayarka a caji ko kuma ka rinka yin surutu
- Ko da ka ga wadanda ka sani kada ka bige da surutu da su
- Idan an kawo maka abinci ko abin sha, kada ka ci kuma kada ka sha
- Kada ka ci wani abu a wajen, misali sweat, chewing gum, ko goro ko makamancin haka
- A lokacin da kake zaune zaman jira kada ka rinka danne-danne a waya
- A lokacin da kake zaune zaman jira kada ka rinka kalle-kalle, ko da kallon TV ne kada ka yi. Zai fi kyau a wannan yanayi ka rinka karanta wani littafi na musamman
- A lokacin da ake maka interview kada ka soki wata masana’antar da ka yi aiki a baya, ko gwamnati, ko wani daban; kada ka soki kowa
- Idan an nuna ba za a dauke ka aikin ba kada ka nuna bacin ranka, duk da haka ka yi godiya
- Kada ka yi karya a CV dinka, wato kada ka saka wani experience ko skill wanda ba ka da shi, ka tabbatar duk abun da yake cikin CV dinka da kuma wanda za ka fada gaskiya ne
- Idan an kira ka office din interview kada ka zauna har sai an ce ka zauna
- Kada ka yi dressing wanda bai dace ba
- Kada ka yi amfani da kalmomin da ba su dace ba, musamman sukar wani ko tabarbarewar kasa, ko matsalar wani yanki ko wani abu makamancin haka
- Kada ka yi latti a lokacin da a ka ce a je, wato kada ka yi African Time, sannan kada ka je da wuri sosai. Misali, idan aka ce 9:00am ne, to ka shiga wajen 9:03am
- Kada ka amsa waya ko kuma ka rinka yawan duba lokaci. Ka tabbatar ka saka wayarka a silence
- Kada ka nuna kana cikin damuwa ko kuma kana matukar bukatar aikin
- A lokacin da kake zaune kada ka yi zaman da ake kira “crossing legs”
- Kada ka nuna ba ka san komai game da ma’aikatar da ka ke neman aiki ba, ka tabbatar ka samu general knowledge kafin ka je
- Ka fada musu specific aikin da za ka yi a kamfanin idan sun bukaci jin haka, ka fada musu irin kokarin da za ka yi, amma kada ka fadi abun da ba za ka iya ba
- Kada ka yi takama da qualifications dinka
- Kada ka je interview ba ka da copies din documents dinka, ka tattara su ka tafi da su a cikin envelope
Ina fatan hakan zai taimaka
Daga Muhammad Auwal Ahmad, CEO Flowdiary
Ku yi sharing wasu ma su amfana.