An samar da Flowdiary a matsayin e-learning platform wato makrantar yanar gizo don koyar da digital skills da harshe Hausa don dogaro-da-kai.

Barka da wannan lokaci mabiya wannan shafi na Flowdiary, shin ko kun san irin zuzzurfan tunanin da aka yi kafin samar da shafinmu kuma makarantarmu ta Flowdiary?

To bari na ba ku bayani. A wannan duniyar da muke rayuwa akwai adadin mutane masu jin yaren Hausa Miliyan Saba’in da Biyar (75,000,000) a bisa hasashen Wikipedia, wanda hasashen ya nuna mafi yawan Hausawan suna rayuwa ne a kasashe kamar haka Nigeria, Niger, Benin, Cameroon, Ivory Coast, Chad, Sudan da kuma Central African Republic.

To acikin mutane Miliyan Saba’in da Biyar (75,000,000), idan aka ce rabinsu wanda adadinsu yayi daidai da Miliyan Talatin da Bakwai da dubu dari biyar (37,500,000), sukan iya fahimtar yaren turanci, to ya ragowar mutanen za su yi, wanda mun sani kusan kowane ilimin fasaha an rubuta shi ne da wannan yare na Turanci. Yi tunani ya ragowar mutane Miliyan Talatin da Bakwai da dubu dari biyar (37,500,000) za su yi, idan su ma suna so duniyar fasaha ta tafi da su?

Wannan dalilin ne ya sa muka samar da makarantar Flowdiary, sannan muka dora darusanmu a shafinmu na yanar gizo, ta yadda kowane mutum zai iya shiga daga ko ina yake a fadin duniya, gami da samar da kwararrun malamai, masu koyar da darussa a bangarorin fasahar zamani wanda daliban wannan makaranta za su koya sannan su dogaro-da-kansu.

3 thoughts on “Me Ya Sa aka Samar da Flowdiary?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *