Android App Development, wato yadda ake gina manhaja ta wayar android, da yadda ake kula da manhajar, da tafiyar da ita a kan tsare-tsaren da aka shirya ta a kai.

Fa’idar da ke tattare ga wannan kwas shi ne gina manhaja ta wayar android ga mutane kamar ‘yan kasuwa da za su na biyanka a duk lokacin da ka gina musu.

Sannan kai ma za ka iya kirkirawa kanka application na wayar android a kan tsari mai kyau da zai taimaka wajen samun maziyarta da za su na amfani da ita kana samun kudaden shigowa.

Kamar yadda ka sani yanzu lokaci ne da ake gudanar da ayyuka a cikin wayoyin hannu, sannan ta hanyar wadannan applications ne ayyuka da yawa ake samun nasarar yinsu a cikin wayarka ta hannu.

Idan ka na son zama kwararre a fannin gina application ta android to makarantar yanar-gizo ta Flowdiary ta tanadar da wannan kwas mai suna Android App Development, wato kwas da zai ba ka damar zama kwararren mai gina manhajar wayar android.

Wannan wani mobile app ne wanda wani ɗalibin Flowdiary mai suna Rislanu Weblearner ya ƙirƙira.

Ko kun san wanne app ne wannan? Chatbot ne wanda za ku iya yin hira da shi, ka tambaye shi abubuwa ya ba ka amsa.

Kafin wannan, Rislanu ya ƙirƙiri apps kala-kala tun a shekarar 2022 bayan ya kammala course ɗin Android App Development a makarantar Flowdiary.

Sannan wadannan wasu daga cikin mobile apps ne wanda daliban Flowdiary suka kirkira a shekarar 2022

Shiga nan ka sauke app dinmu ka yi register don kai ma ka fara koyo yanzu. Da zaran ka yi register sai ka shiga wannan course din mai suna Android App Development for Beginners ka yi subscribing ka fara karatu nan take.

One thought on “Ko Ka San Yadda Ake Gina Android Application da Wayar Hannu?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *