…ga wasu abubuwa guda 7 da ya kamata ka yi

Da farko:

  1. Ka tabbatar ka san abun da kake so ka yi, wato ka kiyasta a ranka me kake so ka yi achieving — shin karance-karance ne, ko koyon skills, ko fara sana’a, ko aure, ko soyayya, ko koyon wani abu daban da sauransu
  2. Ka samu littafi da alkalami ka rubuta su duka, daya-bayan-dayan
  3. Ka mayar da shi kamar to-do list tare da nuna fifiko, misali👇

💠A1 Tasks — koyon skills
—Professional UI/UX Design
—Social Media Marketing
—Smartphone Graphic Design
—Copywriting 101
…..

💠B1 Tasks — karance-karance
—Zo Mu Gina Kamfani na Muhammad Auwal Ahmad
—Rich Dad Poor Dad na Robert Kiyosaki
—Atomic Habits na James Clear
—Tunaninka Kamanninka na Malam Bashir Othman Tofa
…..

💠B2 Tasks — gina kamfani
—Ideation and planning
—Prototype development
—Launching and MVP dev
…..

  1. Kowanne task a cikinsu ka yi masa timing, wato tsawon lokacin da za ka bata a kan shi da kuma yawan abun, misali 👇

💥A1 Tasks — koyon skills
—Professional UI/UX Design (2 months)
—Social Media Marketing (3 weeks)
—Smartphone Graphic Design (1 month)
—Copywriting 101 (3 weeks)
…..

💥B1 Tasks — karance-karance
Zan karanta littatafai guda 12 a wannan shekarar (1 book/month)

💥B2 Tasks — gina kamfani
—Ideation and planning (3 weeks)
—Prototype development (1 month)
—Launching and MVP dev (3 months)

  1. Ka tabbatar za ka fara wannan abun daga yau, sannan kada ka bari sai shekara ta kare kafin ka yi analysis, a’a duk bayan wata daya ka tabbatar ka yi analysis din abubuwan nan. Shin ka samu matsala ko ba ka samu ba?
  2. Ka rinka bin su daki-daki kuma daya-bayan-daya (wato tsarin da ake kira waterfall model)
  3. Ka sauke Google Tasks, Google Keep, da Google Clock a wayarka. Ga amfaninsu nan 👇

i — Google Tasks zai ba ka damar tsara ayyukan da kake son yi daily, weekly ko monthly

ii — Google Clock zai taimaka maka wajen tunasar da kai lokacin da ya kamata ka kwanta bacci da kuma tashi, da ayyukan da ya kamata ka yi a wannan lokacin da sauransu

iii — Google Keep zai ba ka damar storing notes a wayarka, ta yadda za ka iya viewing dinsa a duk wata device da zaran ka daura gmail dinka. Hakan zai ba ka damar rubuta abubuwan da ka yi a wannan ranar, ko satin, ko watan

Rubutawa: Muhammad Auwal Ahmad (CEO, Flowdiary)

Sabuntawa: Flowdiary Webinar, Episode 12

Muna muku fatan nasara. Allah Ya taimaka, amin.

One thought on “YADDA ZA KA TSARA ABUBUWAN DA KAKE SO KA YI ACHIEVING A SHEKARAR 2024”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *