“Role Model” shi ne mutumin da kake mafarkin zama irinsa. Shi ne mutumin da ya je matakin da kake son zuwa. Shi ne wanda kake kwaikwayon tsare-tsarensa.

Wannan mutumin yana da matukar muhimmanci a rayuwarka. Ka bibiyi rayuwarsa.

—Ka binciki me yake yi
—Yaya yake managing time dinsa
—Wadanne littatafai yake karantawa
—Su wa yake kwaikwayo shi ma
—Yaya yake developing ideas
—Mene ne goal, mission, da visions dinsa
—Yaya yake gudanar da rayuwarsa
—Wadanne dabaru yake bi don cimma nasara
—Wadanne irin videos, ko podcasts, ko webinars yake bibiya.

Ba lallai sai ka bi 100% abun da yake yi ba, kuma ba lallai sai ka yi duk abun da yake yi ba (saboda watakila za ka iya samun sabani da shi a wasu ra’ayoyi ko addini.)

Amma yana da matukar kyau ka rinka lura da abubuwan da aka lissafo a sama game da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *