Kafin kawarta ta labarta mata labarin Flowdiary, Khadija Ilyas ta ce tana matukar son ta koyi digital skills amma ba ta samu wanda zai koya mata ba.

Amma bayan ta shigo Flowdiary, ta ce lallai ta zo duniyar da za a share mata hawaye da hannun dama.

Yanzu ta koyi Smartphone Graphic Design, Smartphone Video Editing, da Social Media Management duk da wayarta ta hannu, kuma tana dab da shiga wasu kwasa-kwasan wadanda za su dace da ita.

Babban burin Khadija shi ne ta zama masaniyar na’ura tana zaune a gida, kasancewar inda take babu damar koyon irin wadannan abubuwan da muke yi.

DISCLAIMER: Wannan AI image ne, ba hoton Khadija ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *