Idan mutum bai kasance designer/creator ba — wato mai kirkira, zai rinka tambaya idan ya ga wannan abun: UI/UX. A wannan rubutun mun zo muku da bayani a kansu da kuma bambancinsu kamar haka:

☑ User Interface (UI) Design
Duk wani abun da user/customer zai yi amfani da shi ana son ya kasance a kayace da kyan tsari, yadda zai yi kyan gani a fuska da kuma amfani da shi, wannan shi ake kira User Interface. Don haka duk abun da za a kirkira kamar gida, mota, manhaja, waya, na’ura, jirgi, ko samfurin wani abu ana bukatar a kayata shi da kyan tsari yadda zai yi kyan gani ga mai amfani da shi.

☑ User Experience (UX) Design
Bayan an samu yadda user/customer zai yi amfani da abu bisa duba da kyan tsari, abu na gaba da za a duba shi ne User Experience (UX) wato yadda zai samu saukin yin amfani da wannan abun. Abu mafi muhimmanci shi ne bayan kayan ya kayatu, to tabbas akwai bukatar yadda zai yi sauki wajen amfani da shi. Shin wadanne abubuwa ne aka kawo wadanda za su yi sauki wajen gudanar da wannan kayan.

Kamar yadda kake gani a sama an kawo bayanin wadannan abubuwan UI da UX kuma a nan ka fahimci bambancinsu. Misali: idan muka shigo da sabuwar waya mai suna Flowdiary Phone, abubuwa na farko-farko da za a fara dubawa ko tambaya game da ita su ne kamar haka:

  1. Features
    Wadanne tsare-tsare ne da ita wanda ya dace a ce mutum ya saye ta, wato me ya sa duniya za ta karbi wannan wayar? Tunda daman akwai Android, iPhone, Samsung… da sauransu, to wanne dalili ne za ka sayi wannan sabuwar wayar da na fitar?
  2. User Interface (UI)
    Tunda an samu bayani game da wayar da abubuwan da za ta yi, to yanzu kuma za a bukaci sanin kyan tsarinta. Shin wayar tana da kyau a ido, kuma wadanne kayatawa aka yi mata yadda za ta fi sauran kyau ko makamancinsu?
  3. User Experience (UX)
    Abu na gaba da za a bukaci sani shi ne saukinta wajen gudanarwa. Wato duk yadda abu ya kasance da kyan tsare-tsare da na fuska, amma ba zai samu kasuwa sosai ba matukar ba shi da saukin gudanarwa.

Wadannan fannoni ne da suka shafi bangaren product manager, creators/developers/designers, software engineers da sauransu.

A yanzu haka aka tsaka da neman wadansa suka kware a wannan ilimin na UI/UX Design.

Kai ma za ka iya koya a wajenmu cikin sauki. Sunan course din Professional UI/UX Design a Flowdiary.

Shiga Play Store ka sauke app dinmu mai suna Flowdiary, ka yi register sannan ka shiga wannan course din ka biya kudi N1,800 kacal don ka fara 👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.flowdiary

Invitation code: 7738383

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *