Sanannen dan kasuwar kasar China, shugaban kamfanin Ali Baba mai suna Jack Ma ya kasance mutumin da duniya ba za ta manta da shi ba sakamakon irin gwagwarmayar da ya sha a rayuwa.

—Ya fadi a jarrabawar shiga kwaleji sau 3

—Ya nemi shiga Harvard University sau 10 yana faduwa

—Ya nemi aiki sama da sau 30 amma bai samu ba

Wannan kadan daga cikin abubuwan da yake fada kenan. Amma nasararsa ta fara ne a lokacin da ya je kasar America a shekarar 1994 sannan ya samu ilimin yanar gizo (digital skills)

A nan ya yi tunanin samun damar neman kudi da shi bayan ya kirkiri shafinsa na yanar gizo na farko, inda mutane da dama daga kasarsa ta China suka rinka turo masa sakonni suna so su san wane ne shi, saboda sabon abu ne kirkiran shafin yanar gizo a wajensu.

Jack Ma yana ganin haka ya ce da abokansa tabbas dama ta samu, don haka ya bude team dinsa mai suna China Yellow Pages suna kirkira wa mutane, kamfanoni da gwamnatoci websites suna samun kudi.

A yau Jack Ma shi ne mutumin da yafi kowa tarin dukiya a kasar China sannan daya daga cikin mafi shahararrun mutane a nahiyar Asia da duniya bakidaya.

👉 DARASI – JARIRCEWA
Ba kowa ba ne zai iya irin faduwar da Jack Ma ya yi sannan ya jure. Shi da kansa ya fada; lokacin da aka zo garinsu daukar ma’aikata domin kai su America su 24 ne suka je interview kuma aka dauki 23, shi kadai ne bai samu ba.

Jack Ma ya kasance gwarzo wanda ya jajirce a kan yin abun da ya sa a gaba.

Shi ya sa ake cewa “Jajircewa hanyar nasara ce”

Mu hadu a kashi na biyu…

Daga taskar Muhammad Auwal Ahmad, CEO, Flowdiary, rubutun shekarar 2017

Ku yi sharing wasu ma su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *