Flowdiary ta ba ka damar tsara timetable dinka wanda zai ba ka damar yin karatu a duk lokacin da kake so.

Ga misali na yadda ya kamata ka tsara lokacin daukar karatu, da bibiyar karatu, da kuma yin gwaji (practical).

MUHIMMAN BAYANAI
☑ Saboda kada ka takura wa kanka, za ka iya saita kwana 3 kacal a sati, sannan tsakanin kowacce ranar karatu akwai tazarar kwana 2 na hutu ko wasu hidindimu

☑ A FIRST ROUND an nuna yadda za ka rinka bata sa’a daya kacal kana daukar karatu da safe, saboda safiya lokaci ne wanda kake da nutsuwa sosai kuma babu gajiya

☑ A SECOND ROUND an nuna yadda za ka rinka bata sa’a daya kacal da daddare don yin gwaji (practical) ko bibiyar karatu. Za ka yi wannan aikin ne bayan ka dawo daga hidindimunka sannan ka huta

A shawarce ka kula da wadannan abubuwan 👇

✔ Ka rinka yin jotting a duk lokacin da kake yin karatu

✔ Idan ka fara karatu kada ka yi wani abu daban sai ka kammala

Duk da cewa a Flowdiary darasi ba zai taba wuce ka ba, amma idan ka tsara irin wannan timetable din ba za ka takura wa kanka da yawan ayyuka ba.

Duk da haka idan wannan timetable din bai maka ba, to za ka iya tsara wani naka daban ko ka canja ranakun ko lokutan.

Allah Ya ba da sa’a, amin

Ku fada mana tsarukanku, shin kafin wannan timetable din yaya kuke tsara lokacin karatunku?

2 thoughts on “YADDA ZA KA TSARA LOKUTAN KARATU A FLOWDIARY”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *