- Cristiano Ronaldo ya ce, Na ce wa mahaifina zan zama hamshakin attajiri, amma bai yarda ba. Ga shi yanzu na zama.
☑ Darasi: zuciyarka tana jin abun da bakinka yake furtawa, ka yarda da kanka
- Bill Gates ya ce, Ko kammala karatun digiri ban yi ba, amma na zama hamshakin attajiri.
☑ Darasi: kasancewa kamar Bill Gates ba ya bukatar digiri!
- Lionel Messi ya ce, Ina sayar da shayi don in biya wa kaina bukatuna na cikar burina na zama dan kwallo, ga shi yanzu na zama shahararre.
☑ Darasi: kada ka sare duk rintsi duk wuya. Kada ka bari wani kalubale ya hana ka cikar burinka
- Ben Carson ya ce, Na sha wahala sosai a makaranta, a yanzu kuma na zama daya daga cikin kwararrun likitocin da duniya ta yaba da su
☑ Darasi: kada ka gaji da gwagwarmaya, don hakan alama ce ta yin nasara
- Oprah Winfrey ta ce, An yi min fyade tun ina ‘yar shekaru 9 kacal, amma yau na zama daya daga cikin shahararrun mata a duniya.
☑ Darasi: kada ka bari abun da ya faru da kai a baya ya sare maka gwiwa, tabbas hakan babu abun da zai yi daga kasancewarka wani abu nan gaba
- Nelson Mandela ya ce, An kulle ni a fursuna na tsawon shekaru 27, amma duk da haka bayan na fito na zama shugaban kasa
☑ Darasi: duk irin wahalar da ka sha a rayuwa za ka iya kai wa ga ci, watakila ma matsayin da ba ka taba tunani ba
- Barack Obama ya ce, Duk da kasancewata bakar-fata amma na zama shugaban kasar wata kasa mafi karfin iko a duniya
☑ Darasi: tunaninka kamanninka! Kada ka cire rai da rabo ko kana gabar mutuwa
- Steve Jobs ya ce, Na sha kwana a kasa a dakunan abokaina, lokuta da dama abinci ma ba na iya saya sai dai a ba ni kyauta, amma duk da haka na gina daya daga cikin manyan kamfanonin duniya
☑ Darasi: kasancewarka a karamin matsayi a yau ba shi ke nuna cewa gobe ma za ka ci gaba da kasancewa a haka ba
- Tony Blair ya ce, Malamaina suna cewa ni raggo ne saboda faduwar da nake yi a karatu, amma ga shi yau na zama Prime Minister na United Kingdom
☑ Darasi: kada ka bari kushewar wani a gare ka ya yi tasiri a rayuwarka
- Mike Adenuga ya ce, Har tukin tasi na yi don na biya wa kaina kudin karatu, yau ga shi na zama biloniya
☑ Darasi: jiya daban, yau daban, haka gobe ma daban. Ka sha wahala yau don ka gina gobenka
Daga Muhammad Auwal Ahmad, CEO Flowdiary
Ku yi sharing wasu ma su amfana.