Graphic Design ilimi ne na koyon yadda ake amfani da wayar android ko computer wajen yin ayyukan graphics design kamar banner, logo design, flyer, invitation card, poster, da sauran aikace-aikace na zane da za ka iya yi a cikin wayarka ko computer.

Wadanda suke da kwarewa a fannin graphic design akwai kamfanonin fasaha da gidajen jaridu su na daukarsu aiki domin su na yi masu zanen da zai na fito da shirye-shiryensu a dandulan sada zumunta da mutane za su fahimta ba tare da yin wani dogon rubutu da zai dauki lokaci wajen fahimtar da su ba. Kawai ta hanyar za ne ana iya fito da sakon da ake son isarwa.

Haka nan wadanda suka iya wannan abun suna yi wa mutane da kamfanoni aiki suna biyansu, kamar kirkirar logo, banner, flyer, invitation card da sauransu.

Amfanin graphic design yana da matukar yawa, domin haka wannan bayani na yi ne kawai a takaice.

Sannan a Flowdiary muna da course na Smartphone Graphic Design. Za’a koyar da kai yadda ake yin aikin graphics, kamar kirkirar banner, logo, poster, invitation card, da sauransu ta hanyar amfani da wayarka ta hannu.

Wadannan kadan daga cikin ayyukan da daliban Smartphone Graphic Design suka yi kenan a makarantar Flowdiary

Shiga nan ka sauke app dinmu yanzu ka yi register don kai ma ka fara karatun

One thought on “Smartphone Graphic Design: Koyon Graphics Design da Wayar Hannu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *