About Us | Flowdiary

About Flowdiary

Flowdiary makarantar yanar gizo ce da ke koyar da digital skills kala-kala da harshen Hausa ga dubunnan matasa don su yi amfani da su wajen dogaro-da-kai.


A Flowdiary muna koyar da kwasa-kwasan na'ura da yanar gizo kala-kala irin su Android App Development, Full Stack Web Development, Smartphone Graphic Design, Digital Marketing Mastery, Professional Bug Hunting, Smartphone Video Editing, Social Media Marketing da sauransu cikin sauki.

Flowdiary Team
Flowdiary Team
Saboda a fahimta sosai, muna koyarwa ne da harshen Hausa a shafinmu na yanar gizo, Flowdiary Dashboard da kuma manhajarmu a play store mai suna Flowdiary App. Da zaran dalibi ya yi rajista zai fara daukar darasi a siffar bidiyo, da zaran ya kammala kuma ya sauke shaidar kammala karatunsa, saboda mun tsara darussanmu a siffar bidiyo wanda yake matukar saukaka fahimtar karatu.

Flowdiary Team
A yayin gudanar da taron FlowdiaryKanoMeetup a Bayero University Kano, June 2024
Sakamakon fahimtar cewa tsarin lokaci yana da muhimmanci, babban tsarin da muka fito da shi a Flowdiary shi ne dalibi zai iya rajista a lokacin da yake so, ya dauki darasi a lokacin da yake so, ya kammala karatu a lokacin da yake so, sannan ya sauke shaidar kammala karatunsa a lokacin da yake so.
Flowdiary Team
Yayin da Abdulrahman Muhd, Senior Software Developer dinmu yake karbar shaidar cin gasar da muka yi na Federal Ministry of Youth and Sports Development a Abuja, June 2023

Babban burinmu a Flowdiary shi ne koyar da ilimin digital skills ga dubunnan matasa cikin sauki don su aiwatar da su a zahirance don su samu abun dogaro-da-kai. Hakan zai taimaka musu don gina career a duniyar fasaha wanda zai sa su dogara da kansu har su kirkiro abubuwa.

Flowdiary Team
Muhammad Auwal Ahmad, Chief Executive Officer dinmu yake karbar shaidar cin gasar da muka yi tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe a Damaturu, August 2024

Core Values

  • Koyar da digital skills don dogaro-da-kai
  • Koyarwa a harshen Hausa cikin sauki
  • Koyarwa a araha - kasa da ₦20,000

Awards and Achievements

Our Team

Flowdiary Team

Member 1
Muhammad Auwal Ahmad
CEO
Member 2
Zubairu Said
SWD
Member 3
Abdulrahman Muhd
SSD
Member 4
Abubakar Ibrahim
SGD
Member 5
Ibrahim Auwal
CSA
Member 6
Yasin Abdulwahab Musa
CC
Member 7
Haruna Abdussalam
SMM
Member 8
Nuru Abdulmumin Abdullahi
SMM
Member 9
Salisu Abdulrazak Saheel
Tutor
Member 10
Misbahu Abubakar Bichi
Tutor