Transhumanism

Transhumanism – wani yunkuri ne na kimiyya da fasaha da ake son sabunta mutum, wato a sabunta mutum ya koma salo na 2.0 a madadin tsarin da yake na 1.0 ta hanyar amfani da kimiyya da fasahohin zamani.

Idan har aka yi nasarar sabunta mutum zuwa mataki na 2.0, ana tunanin karfinsa, nazari, basira da saurinsa zai fi na asalin mutanen yanzu da suke a asalin matakinsu na 1.0.