Technological Singularity

Technological Singularity – wannan wani kudiri ne na fasaha da ake ganin akwai lokaci da zai zo inda na’ura za ta mallaki ko ma ta wuce duk wasu fiƙirori, nazari da basira na Ɗan-Adam.

Wannan yunƙuri dai ana tunanin zai iya tabbata a zahiri ne a shekarun 2045, kamar yadda masu hasashe irin Ray Kurzweil suka haƙaito. Masanin ya ce yana tunanin nan da shekarun 2045 Technological Singularity zai iya tabbata a zahiri.

Haka nan wani matashi a ƙasar America mai suna Josh Bocanegra ya ɗaura ɗamarar dawo da mamaci ta hanyar amfani da wannan fasaha. A nashi tunanin, bayan sauƙe bayanan ƙwaƙwalwar mutum zai iya yiwuwa a sanya su a ƙwaƙwalwar saƙago ta yadda shi saƙagon zai iya mu’amala da mutane kamar yadda mamacin ke yi.

Sannan ƙudirin masani kuma attajiri Elon Musk na Neuralink, wani ƙudiri ne na fasaha da kimiyya a inda ake son haɗa ƙwaƙwalwar mutum da na’ura.

Duk waɗannan ƙudirai da yunƙuri ana ƙoƙari ne wajen ganin ko da mutum zai mutu to za a iya adana bayanansa ba tare da asararsu ba.