Machine Learning

Machine Learning ko ML (a takaice) shi ma fasahar na’ura ne da ke ba ta damar koyon abubuwa a maimakon jera mata umarnin abubuwan da za ta yi.

Wannan fasahar ta na’ura ita ke da alhakin ba wa na’ura damar koyon abubuwa kamar yadda mutum yake koya. Tanada kamanceceniya da tsarin koyon mutum da kwakwalwarsa da ita kuma nata tsarin.

A yanzu haka a duniya duk wani babban kamfanin fasaha yana amfani da wannan fasahar domin dacewa da tsarin gudanar da ayyukansa, misali kamfanin Facebook, Google, YouTube Amazon da sauransu.

A cikin ire-iren wannan fasahar akwai:

  1. Supervised Learning – wannan fanni ne inda ake tsarawa na’ura abubuwan da ya kamata ta yi ta hanyar shigar mata da bayanai ko tsare-tsaren na’ura
  2. Unsupervised Learning – a wannan matakin kuwa babu bukatar shigar wa na’ura abubuwanda ya kamata tayi, ita da kanta za ta koya ta hanyar lamakari da abubuwan da suke gudana.
  3. Reinforcement Learning – a wannan tsarin na’ura za ta koyi abu ne ta hanyar gwada mata yadda ake gudanar da wani abu kamar yadda kare ko mage suke koyon abubuwa ta hanyar horarwa da makamantansu.

A wannan fasahar na’ura ana iya yin digiri, mastas har digirin-digirgir a manyan kasashen da suka ci gaba kamar America, China da sauransu.

Related Terms