Internet of Things

Internet of Things – a shekarar 1999 masanin fasaha Kevin Ashton ya samar da sunan wata fasaha, wato wannan fasahar ta ɗaura kayayyakin lantarki akan yanar gizo. Waɗannan kayayyakin lantarkin su kan iya zama firji, fanka, talabijin, mota, da sauransu.

Kamar yadda wayoyin hannu da na’urori suka kasance masu amfani da yanar gizo, a yau ana so su ma waɗannan kayayyakin lantarkin su kasance masu amfani da fasahar yanar gizo.

Cigaban da za a samu shine yin mu’amalar kai-tsaye da waɗannan kayayyaki, kamar umartar fankar gidanka da ta kashe kanta a lokacin da kai ba ka gidan.

Wannan fasaha a yanzu ta samu karɓuwa sosai a faɗin duniya, kuma manyan kamfanoni suna kan gina ta. A yau waɗannan kayayyakin lantarkin sukan iya hawa yanar gizo, ba wai na’ura ko wayar hannu kadai ba.

Shafin Statista ya wallafa cewa zuwa shekarar 2020, dukkanin kayayyakin da aka daura a kan yanar gizo ya kai biliyan 30, inda ake hasashen cewa zai iya kai wai biliyan 75 nan da shekarar 2025.

Further Reading