Artificial Neural Networks ko Neural Networks fasahar na’ura ne da ake yunkuri wajen ganin yanayin nazari da fikirar na’ura ya zama irin na Dan-Adam, ta hanyar kwaikwayon yadda kwakwalwar mutum take aiki.
A wannan sashe masana suna kara kaimi ne wajen tabbatar da tunanin na’ura ya zama irin na mutum, kamar yadda lamarin yake wakana a kwakwalwa.
Wannan fasahar ita ma sashe ce cikin fasahohin Artificial Intelligence.