Artificial Intelligence

Artificial Intelligence, ko AI (a takaice) fasahar na’ura ce da za ta ba wa masanin na’ura damar sanya wa na’ura fikira, nazari, tunani da basira kamar na Dan-Adam.

Wannan fasaha ta samo asali ne daga asalin makirkirin fikirar John McCarthy tun a shekarun 1950’s. Daga nan masana suna shiga binciken yadda zasu iya sarrafa lissafi da sauran ilmuka domin tabbatar da wannan fasaha a wannan zamanin.

Tun farkon wannan karnin na 21 masana suke kirkirar na’urori da sakagai da wannan fasahar. Misali, kamfanin Hanson Robotics ya kirkiri sakagai da dama da fasahar Artificial Intelligence, cikinsu har da shahararriyar sakaguwar nan Sophia wacce tayi suna a fadin duniya. Za ka iya mu’amala da sakaguwar Sophia kamar yadda za ka yi da mutum, duk ta dalilin wannan fasaha.