Time Travel

Time Travel – a takaice shine tafiyar da za a yi don tsallaka wani zamani ko lokaci. Wannan wani kudiri ne na kimiyya da ake son ganin cewa mutum zai iya tafiya zuwa wani wuri, kamar sararin samaniya na dan wani lokaci don tsallaka wani zamani da ba ya son riska.

Irin wannan tafiya ana yinta ne ta wata na’urar tafiyar ta musamman mai suna Time Machine, sai dai har yanzu ba a kirkiri wannan na’ura ba.

Masana suka ce Time Travel ya rabu kashi biyu:

  1. Forward Time Travel – wannan na nufin tafiyar tsallaka wani zamani na gaba, kamar tsallaka shekaru 5 a wannan duniyar ko fiye da haka.
  2. Backward Time Travel – a wannan matakin kuma ana son a yi tafiyar ne zuwa baya, wato a koma shekarun da suka gabata. A nan ana tunanin mutum zai iya komawa baya yayi rayuwa da kakanninsa wadanda suka mutu.

Marubuci Herbert Wells shi ya fara kawo wannan tunanin a matsayin tatsuniya a cikin littafinsa The Time Machine a shekarar 1895.

Related Terms