Windows

Windows – gundarin-tsarin-na’ura ne na kamfanin Microsoft. Windows manhaja ce ta na’ura wacce take taka muhimmiyar rawa a matsayin gundarin-tsarin-na’ura, wato duk wani lamari da zai wakana a cikin na’ura wannan manhaja ce za ta gudanar da shi.

Gundarin-tsarin-na’ura da aka fi sani da Operating System shi ke da alhakin gudanar da duk wani aiki a cikin na’ura. Kowacce irin na’ura akwai nata gundarin tsarin kamar wayar hannu, na’urar tafi-da-gidanka da sauransu.

Wannan gundarin tsarin yana zuwa ne a matsayin manhaja, kamar yadda Windows ta kasance manhaja da ake sa wa na’urori. A yau na’urori sama da kaso 80% ne suke amfani da manhajar Windows a matsayin gundarin-tsarin-na’ura a faɗin duniya, a inda ta zama ita ce ta farko wajen shahara.

Kamfanin Microsoft na babban attajiri Bill Gates, haɗe da abokin aikinsa marigayi Paul Allen sun samar da manhajar Windows ne a shekarar 1983.

Daga cikin manyan gundarin-tsarin-na’ura na duniya akwai Linux, Mac OS da sauransu