Quantum Computer

Quantum computers wadansu irin na’urori ne a ake tunanin zasu zama tsarin ginin na’ura na 6 (6th Generation) nan da shekaru kadan. Wadannan na’urori sun sha banban da kalan na’urorin da ake amfani da su a yau, domin tsarin ma’ajirsu ya sha ban ban – a wadannan na’urorin rumbun bayanai ba ya ajiye bayanai bisa ga haruffan A ko B, 1 ko 0. A maimakon ajiye bayanai a tsarin 1’s ko 0’s da na’urorin yau suke yi, quantum computers zasu adana bayanansu ne ta hanyar amfani da gundarin tsarin kimiyyar quantum.