Mac OS

Mac OS – manhaja ce ta na’ura wacce take taka muhimmiyar rawa a matsayin gundarin-tsarin-na’ura, wato duk wani lamari da zai wakana a cikin na’ura wannan manhaja ce za ta gudanar da shi.

Mac OS ta kasance mallaki kuma ƙirƙirar fitaccen kamfanin fasahar nan na ƙasar America, wato Apple.

Gundarin-tsarin-na’ura da aka fi sani da Operating System shi ke da alhakin gudanar da duk wani aiki a cikin na’ura. Kowacce irin na’ura akwai nata gundarin tsarin kamar wayar hannu, na’urar tafi-da-gidanka da sauransu.

Wannan gundarin tsarin yana zuwa ne a matsayin manhaja, kamar yadda sauransu suka kasance kamar Mac OS. A yau Mac OS ce babbar manhajar gundarin-tsarin-na’ura ta biyu wacce aka fi amfani da ita a faɗin duniya.

Daga cikin manyan gundarin-tsarin-na’ura na duniya akwai Windows, Linux da sauransu.