Linux

Linux – Linux manhaja ce ta na’ura wacce take taka muhimmiyar rawa a matsayin gundarin-tsarin-na’ura, wato duk wani lamari da zai wakana a cikin na’ura wannan manhaja ce za ta gudanar da shi.

Gundarin-tsarin-na’ura da aka fi sani da Operating System shi ke da alhakin gudanar da duk wani aiki a cikin na’ura. Kowacce irin na’ura akwai nata gundarin tsarin kamar wayar hannu, na’urar tafi-da-gidanka da sauransu.

Wannan gundarin tsarin yana zuwa ne a matsayin manhaja, kamar yadda sauransu suka kasance kamar Linux. A yau Linux tana cikin manyan manhajojin gundarin-tsarin-na’ura ta uku wacce aka fi amfani da ita a faÉ—in duniya.

Daga cikin manyan gundarin-tsarin-na’ura na duniya akwai Windows, Mac OS da sauransu.