
Analytical Engine – shine farkon na’urar da aka fara ƙirƙira. Ƙirƙirar masani Charles Babbage wanda ake masa laƙabi da Uban Na’ura, a cikin shekarun 1840’s ya zama babban abun kwatance a duniya.
Analytical Engine ya kasance na’ura ne da ake amfani da shi wajen lissafi, wanda yakeda fiƙirar yi-da-kanka sabanin wadanda suka gabace shi.
Daga wannan lokaci duniyar fasaha ta canja salo na tabbatar da ƙudirin cin nasara wajen ƙirƙirar na’urori wadanda zasu rinƙa tafiya da zamani.