Spyware

Spyware – a na’ura mai ƙwaƙwalwa, spyware wata manhaja ce ta musamman da aka ƙirƙire ta don leƙen asiri wa wasu na’urorin. Ana ƙirƙirar irin waɗannan manhajojin sannan a tura su wasu na’urori domin su gudanar da aikinsu na leƙen asiri.

Leƙen asiri a nan na nuna yadda manhajojin zasu binciko bayanan sirrin mutum a cikin na’urarsa sannan su turawa maƙirƙiransu. An fiye samun irin waɗannan manhajojin ne a yanar gizo, domin su kan zama a cikin na’urar mutum ba tare da saninsa ba.