Software

Software – manhaja ce ta na’ura. Masana tsare-tsaren na’ura suna ƙirƙirar manhaja da za ta ba wa na’ura damar yin wani aiki. A nan, aikin ya kan iya kasancewa lissafi, adana bayanai da sauransu.

Masana tsare-tsaren na’ura suna amfani da wani salo ne na bayanai cike da lissafi da ake ƙira Programming Language, ko yaren na’ura don shirya wa na’ura su don ta fahimci irin aikin da ake so tayi.

Cikin manya kuma sanannun manhajojin da duniya take cin moriyarsu a yau akwai: Adobe Photoshop; manhajar gyara da hada hotuna, Microsoft Office; haɗakar manhajoji na kamfanin Microsoft da suke ba wa mutum damar tsarin rubutu kala-kala, Internet Explorer; manhajar shiga yanar gizo da sauransu.