Programming Language

Programming Languge – a kimiyyar na’ura mai ƙwaƙwalwa, programming language na nufin tsare-tsaren na’ura ko kuma yaren na’ura.

Programming language wani salo ne na lissafi da haɗe-haɗen haruffa har da haruffan alamu, don shigar wa na’ura su akan wani muhimmin aiki da ake so tayi.

Irin waɗanan tsare-tsare sunada yawan gaske a kimiyyar na’ura, wasu ana amfani da su don ƙirƙirar manhaja, wasu shafukan sadarwa na yanar gizo da sauransu. Misalan irinsu akwai Java, PHP, JavaScript, Python, C# da sauransu.

Related Terms