Multitasking

Multitasking – a kimiyyar na’ura, multitasking na nufin gudanar da wasu abubuwa sama da biyu a kai-ɗaya. Maimakon gudanar da abubuwa ɗaya-bayan-ɗaya, wannan salo na multitasking ya kawo tsarin tafiyar da abubuwa da dama a kai-ɗaya.

Kamar yadda gaɓoɓin Ɗan-Adam suke gudanar da abubuwa a lokaci guda kamar ji, gani, magana, tafiya da sauransu, a na’ura wannan salon na fa’idantuwa wajen gudanar da abubuwan da ya ta’allaka da ita kamar jin sauti da yin rubutu – za ka iya sauraron sauti a cikin na’ura a lokaci guda kuma kana rubutu.