Malware

Malware – a na’ura mai ƙwaƙwalwa, malware wata kalar manhaja ce da ake ƙirƙira don turawa wasu na’urorin da niyyar cutar da su.

Wannan manhaja tana cutar da na’ura ta hanyoyi da dama kamar rage mata kuzari, sanya wata manhaja daina aiki, dakatar da wasu sha’anoni ko na’urar ma gaba ɗaya da dai sauransu. Haƙiƙa wannan manhaja ta kasance mai hatsarin gaske. Madatsa ne suke ƙirƙirarta don cimma wata bukatarsu.