Cyber Security

Cyber Security – a sashen na’ura mai ƙwaƙwalwa, cyber security wani fanni ne na ƙwarewa wajen daƙile kutsen na’ura da kayayyakin sadarwa. Wannan fanni na na’ura na taka muhimmiyyar rawa wajen rage yawaitar datse a yanar gizo da duniyar na’ura.

Manyan masana wannan bangaren sun tafi ne kan amfani da iliminsu na ƙirƙirar manhajoji da samar da dabaru don daƙile kutse da ake yi a na’urori. Suna taka rawa wajen daƙile kutsen na’ura, wayar hannu, manhaja, shafin yanar gizo da sauransu.