Algorithm

A kimiyyar na’ura, algorithm tsari ne na bin hanya daki-daki domin warware wata mas’alar na’ura. A nan, mas’ala kan iya zama wani abu da ake son kirkira, misali kirkirar wata manhaja, shafi, gundarin tsarin na’ura da sauransu.

Algorithm yana taka muhimmiyar rawa a duk wani mataki a bangaren na’ura da lisafi. Tsarinsa shine baje yadda gundarin lamarin zai kasance, tun daga farko har zuwa kirkirarsa.

Tarihi ya nuna mutumin da ya fara kirkirar wannan fikirar shi ne Muhammad Ibn Musa al-Khwarizmi, mutumin kasar Persia (yanzu Iraq). Haka nan dai shine makirkirin fikirar lissafin Algebra, wanda ta samo asali a cikin littafinsa al-Kitab al-mukhtasar fi hisab al-jabr wa’l-muqabala.