flowdiary cryptocurrencyflowdiary cryptocurrency

Cryptocurrency wani nau’in kasuwanci da hada-hadar kudi ne da yake gudana a yanar-gizo ta hanyar yin cinkayya da hulda da kudaden da suke ba a zahiri ba, wato kudaden yanar-gizo kamar bitcoin, litecoin, dogecoin, ethereum, da sauransu. A yanzu haka kasuwancin cryptocurrency ya mamaye kusan ko ina a duniya, kasashe da dama sun rungumi tsarin harkokin hulda da kudaden na yanar-gizon.

Fa’ida da ke tattare da amfani da kudeden yanar-gizo na cryptocurrency shi ne yadda bayan ka mallake su wato sayensu a kusuwannin yanar-gizo da ake hada-hadarsu, sannan kuma kai ma za ka iya sayar da su a lokacin da farashinsu ya yi sama a kasuwarsu.

Wannan babban cigaba ne da duniya ta samu a yau sakamakon yadda hasashen masana yake tabbatar da cewa a nan gaba kadan kudaden da muke da su a zahiri za su yi karanci, za a dawo yin harkoki da irin nau’o’in kudaden yanar-gizo na cryptocurrency.

Daga cikin fa’idar da ke tattare da cryptocurrency akwai damar yin sayayya a shagunan yanar-gizo ta hanyar biyansu da nau’in kudin na cryptocurrency.

Sannan daga karshe zan son ka fahimci cewa a makarantar yanar-gizo ta Flowdiary an tanadar da kwas din cryptocurrency da ake koyar dabaru da hanyoyin fara kasuwancin cryptocurrency, da yadda ake sayen coins, da irin coins da ya dace ka saya wadanda ake da kyakykyawan zaton hauhawar farashinsu a nan gaba.

One thought on “Me Kake Son Sani Game Cryptocurrency: Bayani da Kuma Fa’idarsa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *