Mun kawo tsarin Points da Batch a Flowdiary, ga bayanansu kamar haka:


Points

Points wani maki ne da ɗalibi yake samu a Flowdiary a duk lokacin da ya yi comment (tambaya) ko kuma ya amsa tambayar wani, ko liking lecture, ko bibiyar comments, ko yin review a course ɗinsa, ko enrolling sabon course. Ana amfani da Points ɗin ɗalibi wajen gane yanayin yadda yake mayar da hankali a karatu. Idan mutum yana samun Points da yawa hakan zai sa a ba shi kyauta.

Badge
Shi kuma Badge shi ne matakin da dalibi ya kai a yayin da yake karatu a Flowdiary. Matakin ɗalibi yana hawa ne a duk lokacin da yake samun Points da yawa. Matakan Badge su ne kamar haka:

  1. Learner – 0-50 points
  2. Amateur – 51-100 points
  3. Creative – 101-150 points
  4. Hardworking – 151-250 points
  5. Researcher – 251-300 points
  6. Skillful – 301-400 points
  7. Strategist – 401-500 points
  8. Master – 501-600 points
  9. Champion – 601-750 points
  10. VIP – 750-1000+ points

Shin me ɗalibi zai samu idan ya tara Points?
Kasancewar burinmu shi ne koyar da digital skills don dogaro-da-kai, muna shirin kawo wani tsari mai suna Flowdiary Jobs, wani sashe wanda ɗalibi zai iya neman aiki daga kamfanoni da manyan mutane.

Duk wani ɗalibi yana buƙatar ya samu aƙalla points 101 zuwa sama, wato da zaran ya shiga matakin Creative Badge, to daga nan za a ba shi damar cika gurbin neman aiki.

Kenan Points zai yi wa ɗalibai amfani ne wajen neman aiki da kuma samun kyaututtuka.

Ku yi updating sabon app ɗinmu don morar waɗannan sababbin tsare-tsaren

One thought on “Mene ne Amfanin Points da Badge a Flowdiary?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *