WordPress wata manhajar yanar-gizo ce da ake amfani da ita domin kirkirar shafin yanar-gizo ba tare da an yi amfani da yarukan na’ura ba. Sannan kuma har a iya daidaita tsarukansa, da bunkasa shi, da kuma kula da shi.

Za ka iya kirkirar shafin yanar-gizo na tallata kasuwanci, kawo labarai, ilimantarwa, fadakarwa, ko nishadantarwa ta hanyar amfani da manhajar WordPress. Ko kuma ka kware wajen kirkirar shafin ga ‘yan kasuwa, marubuta, da masu sana’o’i da za ka rinka kirkirar masu su na biyanka.

A Flowdiary akwai kwas sukutum da za ka koyi yadda ake gina shafin yanar-gizo na WordPress, da yadda za ka kula da shi, ingantashi, da kuma bunkasa shi ta yadda zai na samar maka kudeden shigowa.

2 thoughts on “WordPress: Yadda Za Ka Gina Shafin Yanar-gizo ba Tare da Yaren Na’ura ba”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *