Social Media Marketing ya na nufin hanyar da ake tallata wata haja, kasuwanci ko sana’a a dandulan sada zumunta na yanar-gizo, kamar su Facebook, WhatsApp, Instagram, Tiktok, Telegram, Twitter, da sauransu.

Kamar yadda akwai mutane da dama da suke son yin talla a dandulan sada zumunta domin samun abokan ciniki, sai dai da yawa daga cikinsu ba su san yadda ake amfani da dandulan sada zumuntar ba wajen tallata hajarsu ko bunkasa kasuwancinsu. Saboda haka a wannan kwas na Social Media Marketing za a koyar da kai duk wasu hanyoyi da dabaru da za ka yi amfani da su ka tallata kasuwarka ko sana’arka a shafuka ko dandulan sada zumunta.

Daga cikin abubuwan da Social Media Marketing ya ke koyar da mu sun hada da: yadda ake creating content domin tallata kasuwa, yadda ake understanding audience, anatomy of social media post, yadda ake zabar social media network da za’a yi kasuwanci da shi, ma’nar brand identity, da sauransu.

Za ka iya samun wannan kwas na Social Media Marketing a manhajar karatu ta Flowdiary, sannan ka yi register da shi a kan farashi mai sauki ka fara Karatunka.

2 thoughts on “Koyi Social Media Marketing Don Sanin Dabarun Tallata Hajoji a Dandulan Sada Zumunta”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *