TAMBAYOYI DA AMSOSHINSU GAME DA MAKARANTAR FLOWDIARY ACADEMY

Q1: Mene ne Flowdiary Academy?
Ans 1: Flowdiary Academy makarantar yanar gizo ce da ke koyar da digital skills da harshen Hausa don dogaro-da-kai kamar Web Development, Android Development, Graphic Design, Cyber Security, Bug Hunting, Digital Marketing, Photoshop da sauransu

Q2: Ta yaya zan shiga wannan makarantar?
Ans 2: Mai sauki ne, duk wanda ke son shiga wannan makarantar zai yi rajista ne ta hanyar shiga wannan link din: https://flowdiary.com.ng sannan sai ka shiga Enrol, inda za ka cike bayananka tare da biyan kudin rajista bayan ka gama

Q3: Nawa ne kudin shiga
Ans 3: Ya danganta ga kwas din, saboda akwai kwasa-kwasai da dama kuma kowanne akwai kudinsa

Q4: A ina ake yin darasi?
Ans 4: Idan kana da wayar Android za ka iya sauke application din mu na daukar darasi, bayan ka gama rajista sai ka shiga app ka yi login sannan ka fara daukar darasi. Idan kuma wayar iPhone ko computer gare ka, za ka shiga shafinmu tare da yin login sannan ka fara daukar darasi

Q5: Yaushe za a fara darasi?
Ans 5: Duk wani bayani game da fara karatu, kayan karatu, sauke application, shiga portal da sauransu za a same su a Telegram: https://t.me/flowdiary, don haka ka yi joining a nan za ka rinka samun duk wani bayani

Q6: Yaushe ake yin karatu?
Ans 6: Ana yin karatu da daddare, kuma kowanne course ana yin karatunsa sau biyu a sati

Q7: Yaya tsarin daukar darasi yake?
Ans 7: Duk wani darasi a siffar video yake, za ka shiga ka kalla sannan ka yi jotting a littafinka

Q8: Ana bayar da certificate idan an gama?
Ans 8: eh, ana bayar da certificate idan an gama karatu duka

Q9: Tsawon wane lokaci ne karatun?
Ans 9: Ya danganta ga course din, wani 3 weeks, wani kuma 4 weeks ko 5 weeks

Q10: Zan iya rajistar course sama da daya?
Ans 10: eh, za ka iya rajistar course har guda 3

Idan kana da wata tambayar ka tura mana ta WhatsApp 2348162374764

Bibiye mu ta Telegram da Facebook:

—Telegram: https://t.me/flowdiary

—Facebook: https://fb.me/flowdiary

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *