Reproduction

Reproduction lamari ne na haihuwa, wato lamari ne da ya hada da jima’i da daukar ciki da haduwar kwan mace da maniyyin namiji da makamantansu. Reproduction yana faruwa a kan kowacce halitta kama daga dabbobi, mutane da tsirrai.

Ovulation

Ovulation lamari ne na fitar ƙwai daga masarrafar mace. Lamarin ovulation yana faruwa kafin fertilization, wato fitar ƙwai daga masarrafar mace zuwa haɗuwarsa da maniyyin namiji.

Abunda bincike ya nuna shi ne kowace mace ana haihuwarta da ƙwai aƙalla miliyan 2, amma da zaran ta fara girma su ma za su fara lalacewa. Idan kuwa ta balaga, akan samu aƙalla ƙwai 500,000 a masarrafarta.

Hakanan idan tana tsufa za su yi ta lalacewa, wannan dalilin ya sa da zaran mace ta manyanta ba za ta iya haihuwa ba sakamakon rashin ƙwan da take da shi.

Fertilization 

Fertilization wani lamari ne da ke faruwa a lokacin da ƙwan mace da maniyyin namiji suka haɗu don fasalta yadda za su samar da ɗa. A wannan lamari na haɗuwarsu shi ake ƙira fertilization, zuwa gaba kuma ya koma zygote, wanda shi ne lamari na gaba wajen gudanar da samuwar ɗa.

A kan iya gane mace na da juna biyu lokuta kaɗan bayan faruwar wannan lamari na fertilization, a inda wasu alamomi da za a iya gani suka haɗa da:

  • Ɓacewar al’ada
  • Kasala
  • Zafin jiki (zazzabi)

Gamete

Gamete su ne ƙwayoyin haihuwa waɗanda ke haɗuwa da juna yayin fertilization. Gamete din mace shi ake kira kwai, na namiji kuma maniyyi. Wanann haduwa ta mabambantan gametes shi ke samar da zygote, wanda daga nan ne

Zygote

Zygote shi ne cell da aka samar lokacin da gamete biyu suka haɗu yayin fertilization. A samuwar mutum, da zaran ƙwan mace da maniyyin namiji sun haɗu yayin fertilization, shi kuma a lokacin zygote yake samuwa. Zygote yana samuwa ne da zaran lamarin fertilization ya auku.

Pollination

A game da samuwar tsirrai, pollination lamari ne na fitar ƙwayar pollen daga jikin tsirrai namiji zuwa ƙofar tsirrai mace. Wannan lamari na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke ba wa tsirrai damar samar da wasu tsirrai. Ba tsirrai kadai ba, wasu kwari suna amfani da wannan siga wajen haihuwa kamar kudan zuma.

Iren-iren Pollination

  • Cross-pollination –wannan ne inda ƙwayar pollen ta namiji take fita ta shiga ƙofar tsirrai mace daga wani fure
  • Self-pollination –wannan kuma babu buƙatar wata mace a kusa, da zaran ƙwayar pollen ta fita za ta iya sauƙa a kofar namijin.

Kasancewar rashin sha’awa a jikin tsirrai, pollination yana faruwa ne a duk lokacin da iska ta kaɗa, daga nan ƙwayar pollen idan ta fita ta kan sauƙa a duk inda ta samu. Kakanan ƙwari su kan shigar da wannan mu’amaka a tsakanin tsirrai.

Madogara

[1] Biology> Reproduction > References