Optic Nerve

Credit: MedGadget.com

Layin sadarwa da ya haɗa ido da ƙwaƙwalwa don isar da saƙo, a harshen Hausa ana ƙiransa jijiyar ido. Wannan layin sadarwa da ke kula da duk wani abunda mutum yake kallo yana daukar saƙon ne ya kai ƙwaƙwalwa ta yadda ƙwaƙwalwa za ta iya fahimtar me ido ya kalla.

A duk lokacin da layin sadarwa Optic Nerve ya samu matsala sai idon mutum ya fara ciwo, wasu lokutan ya rasa gani ko fahimtar launi a wannan idon.

Wasu matsaloli da ke samun layin sadarwan sun haɗa da:

  • Optic Nerve Atrophy – wannan matsalar ta kan sa mutum ya rasa gani
  • Optic Neuritis – wannan kuma lalata layin sadarwan yake gaba ɗaya, ta yadda mutum zai iya rasa ganinsa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba
  • Optic Nerve Hypoplasia – wannan matsalar kuma ta kan samun mutum tun lokacin haihuwa ko kafi haka, mafi yawancin lokuta ma akan haifi mutum da ita. Masana suka ce abubuwan da ke janyo matsalar sun haɗa da rashin kai wa lokacin haihuwa ko ciwon siga daga wurin mahaifiya.

Karanta:

Madogara

[1] Biology> Optic Nerve > References