Nervous System

Saboda kowane sashi a jikin mutum yana haɗe da ƙwaƙwalwa ta yadda yake saurin kai mata sako, Nervous System shi ke aiki haɗa kowane sashe na jikin mutum da ƙwaƙwalwa.

Abubuwan Da Suka Samar Da Nervous System

  • Ƙwaƙwalwa – ƙwaƙwalwa ita ce a farko saboda ita ake kai wa saƙonni, kuma ita take bayar da saƙonni a dawo da su sashina.
  • Ƙashin baya – ƙashin baya da ake ƙira Spinal Cord shi ne ya haɗa waɗannan sashinan sadarwan da ƙwaƙwalwa
  • Layukan sadarwa – duk wani sashe na jikin mutum yana buƙatar layin sadarwa don kai wa ƙwaƙwalwa saƙo, a nan layukan sadarwa suna taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙonnin zuwa na’ura.

Ire-iren Layukan Sadarwa

Kowane layin sadarwa da ke kai saƙo ko ya karɓa daga gaɓɓai ko sashina a jikin mutum yana da irin nashi aikin, kamar haka:

  • Sensory Nerves – waɗannan sashinan sadarwan suke ɗaukar saƙonnin su kai ƙwaƙwalwa, musamman lamuran da ba su faru a jikin mutum ba, kamar ganin abu da ido, ko sauraron sauti lamura ne da suke bukatar kusanci da jikin mutum domin samun kusantarsu, amma ba don taba su ba. Sensory Nerves su ke ɗaukar irin waɗannan saƙonnin da mutum ya gani ko ya saurara zuwa cikin ƙwaƙwalwa.
  • Motor Nerves – waɗannan kuma su ke isar da lamuran da ke faruwa a duk wani sashi ko gaɓɓai a jikin mutum, kamar ji, motsi, da sauransu.

Karanta:

Madogara

[1] Biology> Nervous System > References