Immune System

A kowane lokaci cututtuka su kan iya kai wa mutum hari, musamman ƙananan ƙwayoyi kamar su bacteria ko parasite. Don haka Immune System da ake ƙira garkuwan jiki shi yake yaƙar su sannan ya fattake su a duk lokacin da ya fi ƙarfinsu saboda kada su cutar da mutum.

Bayani

  • Duk lokacin da wata cuta ta shiga jikin mutum garkuwar jikin mutum zai sanya dakaru don yaƙarta, idan suka yi nasara za a murƙushe cutar, idan kuma aka samu matsala cutar za ta kafa sansaninta
  • Abunda ake ƙira rigakafi shi ne horar da garkuwar jikin mutum don gane baƙo da wuri, kamar cuta saboda kada ta fara kafa sansani a jikin mutum
  • Rashin yin bacci yana hana garkuwar jikin mutum gudanar da aikinta yadda ya kamata, haka nan yawan yin bacci ko rashin ware jiki yana sa ta rashin kuzari

Karanta:

Madogara

[1] Biology> Immune System > References