Evolution

Evolution a kimiyya na nufin canje-canjen cigaba na halittu har zuwa matakin kasantuwarsu na ƙarshe. Evolution ya nuna yadda biri ya rinƙa canje-canjen cigaba har zuwa matakin ƙarshe na kasancewa mutum, haka nan sauran halittu.

Bayani

  • A kan iya kiran kalmar evolution da tadawwuri a harshen Hausa, duk da kalmar ta samo asali ne daga harshen larabci
  • Bincike kan DNA ne ya ƙara wa masana haske kan evolution
  • Samuwar mutum zai iya jinginewa zuwa shekaru miliyan 5 da suka gabata
  • Charles Darwin, masanin kimiyyar halittu da yayi bayani a kan evolution, ya shafe aƙalla shekaru 20 kafin ya gama rubuta littafin da yayi bayani a ciki On the Origin of Species
  • Dacewa da wuri ya kan sa halitta samun wasu ‘yan canje-canje da har ya kan kai ta ga samuwar wasu nau’in halittun

Evolution ba kai tsaye yake nuna canjin halitta ba, wasu lokutan canjin yanayi da dacewar wurin rayuwa yana sanya halitta samun wasu ‘yan canje-canje na siffa don dacewa da ka’idar halitta.

Madogara

[1] Biology> Evolution > References