Dinosaurs

dabbobin dinosaurs

Dinosaurs wasu dabbobi ne da suka rayu na tsawon shekaru miliyan 245, kuma sun halaka shekaru miliyan 65 da suka gabata. Waɗannan dabbobi masu kama da ƙadangare suna da girman gaske. Masana kimiyyar binciken tarihi sun haƙaito cewa dutsen asteroid ne ya kawo ƙarshensu.

Bayani

  • Sun rayu tsawon shekaru miliyan 245 a duniyar Earth
  • A shekarar 1842 wani masanin kimiyyar halittu da ake ƙira Sir Richard Owen ya samar da wannan suna daga lalmar Greek deinos wacce ke nufin “tsoro” da kuma sauros wacce ke nufin “ƙadangare”
  • Akwai aƙalla nau’ukan waɗannan dabbobi 700, amma ba duka ba ne suka halaka
  • An samu ƙwarangwal ɗin waɗannan dabbobin ne a kowacce nahiya da ke duniyar Earth, kuma saboda girman ƙwarangwal ɗin hakan ya tabbatar lallai waɗannan dabbobi ba ƙaramin girma gare su ba.
  • A manyan gidajen tarihi akwai ƙwarangwal ɗinsu, masana ne suka kai bayan sun gama wasu ‘yan bincike-bincikensu a kai.

Madogara

[1] Biology> Dinosaurs > References